✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Sako Seaman Abbas Bayan Shekaru 6 A Tsare

Rundunar sojin Najeriya ta kori Seaman Abbas Haruna daga aiki bayan ta tsare shi tsawon shekaru shida,

An saki  sojan ruwan Najeriya da ake daure da shi na tsawon shekaru shida, mai suna Seaman Abbas Haruna, wanda matarsa ta kai koke a shirin Barekete Family na kafar yaɗa labarai na Human Rights.

A safiyar Juma’a Saeman Abbas da matarsa Hussaina sun bayyana a cikin shirin na Brekete Family, inda matarsa ta sanar cewa sojoji “sun kori shi daga aiki.”

An hango Seaman Abbas tare da matarsa a cikin dakin gudanar da shirye-shirye na Human Rights Radio (Berekete Family) a safiyar yau.

Sai dai har kawo  wannan lokacin, Rundunar Sojin Najeriya ba ta fitar da sanarwa a kan korar jami’in ba, kamar yadda ta saba.