✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake nada Sheikh Sudais Shugaban masallatai biyu mafi girma a Saudiyya

An sake nada Sheikh Abdul Rehman Al Sudais, a matsayin Shugaban manyan masallatan nan guda biyu a kasar Saudiyya domin kula da wuraren biyu mafi…

An sake nada Sheikh Abdul Rehman Al Sudais, a matsayin Shugaban manyan masallatan nan guda biyu a kasar Saudiyya domin kula da wuraren biyu mafi daraja a Musulunci.

Kamar yadda wata sanarwa daga shafin Facebook na Masallatan Haramin – biyu – mai suna Haramain Sharifai’s Facebook page, sake nadin nasa na kunshe ne cikin wata oda daga masarautar kasar ta bayar – wacce ‘Sarki Salman mai kula da Masallatan ya fitar.’

Sanarwar ta ci gaba cewa, Sheikh Sudais din zai sake jagorantar al’amuran masallatan biyu na wasu shekara hudu masu zuwa.

Sheikh Al-Sudais, dai ya kasance yana shugabancin kula da masallatan ne tun ranar 8 ga watan Mayun 2012, kuma shi ne Babban Limamin Masallacin Harami na Makkah.