✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake lalata mutum-mutumin Lionel Messi

A karo na biyu wadansu bata-gari da ba a gano ko su wane ne ba, sun sake lalata mutum-mutumin shahrarren dan kwallon Ajantina Lionel Messi.…

A karo na biyu wadansu bata-gari da ba a gano ko su wane ne ba, sun sake lalata mutum-mutumin shahrarren dan kwallon Ajantina Lionel Messi.

Mutum-mutumin, wanda aka girke a babban birnin kasar Ajantina Beunos Aires an yi shi ne a watan Yunin 2016 amma ya zuwa wannan lokaci, wasu batagari sun lalata shi sau biyu ba tare da sani dalili ba.

Kamar yadda rahoton da jami’an tsaro na ’yan sandan kasar Ajantina suka fitar, sun ce har yanzu ba a gano dalilin da ya sa ake yawan lalata mutum-mutumin dan kwallon ba.

Idan za a tuna Messi ne ya taimaki Ajantina hayewa gasar cin kofin duniya da zai gudana a Rasha bayan ya zura kwallaye uku a ragar Ecuador a wasan karshe na neman hayewa gasar a watan Oktobar bana. An ce batagarin sun samu nasarar guntule kai da kafafuwan mutum-mutumin Lionel Messi ne kuma har yanzu ba a samu nasarar kama ko gano dalilin da ya sa suke yin haka ba.

A watannin baya an taba lalata mutum-mutumin amma mahukunta kasar suka gyara sai ga shi a karo na biyu an sake lalatawa.