Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan awaren Biyafara ne na IPOB, sun kone wani ofishin ’yan sanda na yankin Atta da ke Karamar Hukumar Njaba a Jihar Imo.
Kazalika, ’yan ta da zaune tsayen sun kuma kone Kotun Majistire da wata Babbar Kotu a yankin na Atta tare da lalata wata cibiyar kiwon lafiya.
- Chelsea da City za su fatata a wasan karshe na Kofin Zakarun Turai
- An kashe mayakan Boko Haram 10 a garin Rann
Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne tsakanin karfe 1 na dare da kuma 2 na daren ranar Asabar.
Majiyar rahoton ta ce maharani sun kwashe tsawon sa’a biyu suna harbe-harbe kan mai uwa da wabi kafin cinna wa gine-ginen wuta.
Sai dai yayin da aka tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, Bala Elkana, ya ce ba a sanar da shi game da faruwar lamarin ba.
A watannin baya bayan nan dai masu fafutikar neman kafa yankin Biyafara sun matsa kaimi wajen kai hare-hare a Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudancin Kasar.
A ranar Asabar ce ’yan awaren Biyafara suka sanya dokar hana fita wacce ta tilasta mazauna Jihar Imo kasancewa a gidajensu.