✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sake damke fursunoni 551 da suka tsere daga kurkukun Kuje

Akwai ragowar fursunoni 328 da har yanzu ake nema ruwa a jallo

An sake damke akalla mutum 551 daga cikin fursunoni 879 da suka tsere sakamakon harin da aka kai gidan gyaran hali na Kuje da k Babban Birnin Tarayya Abuja a Talatar da ta gabata.

Ya zuwa hada wannan labari, akwai ragowar fursunoni 328 da ake nema ruwa a jallo don a sake damke su.

Yayin harin, wasu mutum hudu daka cikin fursunonin da kuma jami’in NSCDC daya suka rasa ransu, yayin da mutum 16 suka ji rauni ana kuma ci gaba da yi musu magani.

Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Kasa ta ce, ana ci gaba da kokarin ganin an sake kamo ragowar fursunonin da suka tsere baki daya.