✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake ƙara kuɗin fetur a gidajen man NNPC

Gidajen man NNPC sun ƙara kuɗin fetur a karo na biyu cikin makonnni uku, duk kuwa da fara aikin Matatar Ɗangote

Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya ƙara farashin man fetur a karo na biyu cikin makonnni uku.

Aminiya ta lura cewa gidajen man NNPC sun kara farashin litarsu zuwa N1,020 a Jihar Legas, a Abuja kuma zuwa N1,050.

Wakikinmu ya lura cewa gidan man NNPC da ke titin Arab a unguwar Kuwa da ke Abuja, ya fara sayar da fetur a kan sabon farashin.

Kafin wannan ƙarin, ana sayar da litar man fetur ne a  kan N897 a Abuja, a Legas kuma N885; amma a ranar 9 ga watan Oktoba da muke bankwana da shi aka ƙara na Legas zuwa N998, na Abuja kuma zuwa N1,030.

An yi waɗannan karin kuɗin man fetur a watan Oktoba ne, duk da fara aikin Matatar Man Ɗangote, wadda ake tunanin za ta kawo sauki da wadatuwar man a ƙasar.

Tuni dai NNPC ya janye kansa a matsayin mai dillancin mai tsakanin Matatar Ɗangote da ’yan kasuwa, inda aka ba su damar yin ciniki da kamfanin.

Hakan ne a nufin NNPC yabtsame kansa daga matsayin da ya saba na biyan cikin N133 a kan kowane litar fetur da ’yan kasuwar ke saya, wanda aka fi sani da tallafin mai.

Masana sun yi gargadi cewa wannan mataki na nufin NNPC ya tsame kansa daga lamarin gudanar da farashin man a Nijeriya.

Ana fargabar cewa matakin na iya kaiwa ga ’yan kasuwan suna cin karensu babu babbaka wajen ƙayyade farashi.

Tun kafin yanzu, Aminta ta ruwaito yadda masu ababen hawa suka yi watsi da su, suka koma hawa na haya, saboda tsadar fetur.

Gidajen mai da dama sun koka kan rashin ciniki a sakamakon raguwar adadin man da masu ababen hawa ke saya.

Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa wasu masu ababen hawa sau ɗaya suke shan mai a wata, kuma akasarin mutane sun daina cika tankokinsu.