Wasu mutane da ake kyautata zaton masu garkuwa ne domin neman kudin fansa sun sace dan wan tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Rahotanni sun nuna cewa iftila’in ya sami Musa Abdullahi, wanda aka fi sani da Yaya Baba ne a kan hanyarsa ta komawa Kano a hanyar Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata.
- An yi garkuwa da matar basarake a Kano
- Sanusi ya sha kaye a kotu
- An kama magidancin da ya yi garkuwa da kansa a Kano
“Iyalan sun yi kokari wajen tattara kudaden, amma lokacin da wanda aka tsara zai kai musu kudin ya tafi sai wayarsu ta daina shiga kwata-kwata; har yanzu ba mu sake jin duriyarsu ba”, inji majiyar Aminiya.
Ya zuwa yanzu dai Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba, amma wasu majiyoyi sun ce iyalan wanda aka sace din ne ba su yarda a yayata labarin ba tun da farko.
Majiyar wacce ke da kusanci da iyalan tsohon sarkin ta kuma shaida wa Aminiya cewa masu garkuwar sun tuntube su domin neman kudin fansa, ko da yake bai bayyana ko nawa suke nema ba.
Ta ce tuni iyalan suka fara neman kudin, amma kuma daga bisani sai suka rasa lambar masu garkuwar.
Babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja dai ta yi kaurin suna a ’yan shekarun nan wajen ayyukan masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma fashi.
Duk kuwa da kokarin da Gwamnatin Tarayya ta ce tana yi ba dare ba rana wajen yaki da su, da alama har yanzu akwai sauran rina a kaba.