✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sa dokar takaita fita a Kajuru da Chikun

Ashekaranjiya Laraba ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta saka dokar takaita fita a kananan hukumomin Kajuru da Chikun da ke jihar. A cewar gwamnatin, dokar takaita…

Ashekaranjiya Laraba ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta saka dokar takaita fita a kananan hukumomin Kajuru da Chikun da ke jihar.

A cewar gwamnatin, dokar takaita fitar ta shafi garuruwan Kujama da Marabar Rido da ke Karamar Hukumar Chikun.

Babu wani dalili da gwamnatin ta bayar na takaita fitar, wadda ta ce za ta fara aiki ne daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kakakin Gwamnan Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ta ce dokar takaita fitar za ta ci gaba da gudana har zuwa wani lokaci nan gaba.

Ya kuma ce an bai wa jami’an tsaro umarnin tabbatar da jama’ar yankin sun bi dokar.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga jama’ar da ke zaune a inda dokar ta shafa su yi hakuri da halin da suke ciki, tare da bin umarnin jami’an tsaro.

Idan ba a manta ba, a ranar Lahadin da ta gabata ce wadansu ’yan bindiga suka kashe mutane sama da goma a Unguwar Barde da ke Karamar Hukumar Kajuru.

Rundunar ’Yan sandan Jihar ta bakin Kakakinta Yakubu Sabo, ta tabbatar da mutuwar mutum 16 sha a harin na Unguwar Barde. Kuma ta ce rundunar tana iya kokarinta wajen gano masu hannu a wannan hari da nufin gurfanar da su a gaban kotu domin hukunta su.