✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rusa gidaje sama 50 na al’ummar Narkuta

A ranar Asabar da ta gabata ce wadansu ma’aikata tare da kariyar jami’an tsaro daga Jami’ar Jos, suka rushe gidaje sama da 50 a na…

A ranar Asabar da ta gabata ce wadansu ma’aikata tare da kariyar jami’an tsaro daga Jami’ar Jos, suka rushe gidaje sama da 50 a na al’um,ar garin Narkuta da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.

Idan ba a manta ba, mako biyu da suka gabata Aminiya ta ruwaito rikicin da ya faru a garin na Narkuta, wanda ya yi sanadin rasa ran mutum daya, kan takaddamar mallakar fili a tsakanin Jami’ar Jos da al’ummar garin Narkuta.

Da yake zantawa da ’yan jarida a fadarsa da ke garin Narkuta Sarkin Narkuta Injiniya Muhammad Bello ya bayyana takaicinsa kan faruwar wannan al’amari. Ya ce a safiyar ranar Asabar, suka tashi suka ga jami’an tsaro, sun kewaye su tare da ma’aikata daga Jami’ar Jos da motocin rushe gini suka fitar da mutane daga gidajensu suka kama rushe gidajen.

Ya ce, “Wannan abu da aka yi mana an take mana hakkinmu na dan Adam, an rusa mana gidaje sama da 50. A matsayinmu na masu son zaman lafiya da bin doka da oda, muna bin dukkan hanyoyin da suka kamata, wajen ganin an warware wannan takaddama  kan mallakar wannan fili. Don haka muna kira ga masu ruwa- da-tsaki kan wannan al’amari, na ciki da wajen Jihar Filato su dubi wannan abu da aka yi mana, na rushe mana gidaje wanda ya jefa iyalanmu cikin mawuyacin hali, don warware wannan takaddama.”

Lokacin da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Jami’ar Jos, Abdllahi Abdullahi don jin ta bakinsa kan lamarin, ya ce ba zai iya cewa komai ba, domin yanzu yana hutu.

Jami’ar Jos da al’ummar garin Narkuta dukkansu suna ikirarin cewa su suka mallaki wannan fili da ake takaddama a kai, wanda al’ummar garin na Narkuta suka yi gine-gine a kai.

A wata sanarwa da al’ummar garin na Narakuta suka fitar, sun ce sun sayi filin ne daga Kamfanin Ron Properties Nig Ltd a madadin Iyalan Wakili Jatau da suka ba shi hakkin sayar da filin da su ne asalin suke da mallakarsa.

A yayin da ita ma a wata sanarwar da ta fitar dauke da sanya hannun Mataimakin Babban Magatakardar Jami’ar Jos, Wilson Yale, jami’ar ta bayyana cewa Jami’ar Jos  ta sayi wannan fili ne daga Kamfanin Yin Jan Bulo na Nigeria Bricks and Clay Product Ltd ta hannun Kamfanin Sayar da Kadarorin Gwamnatin Tarayya (BPE).