✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da shugabannin Kungiyar Muryar Talaka na Katsina

A ranar Lahadin da ta gabata ce Kungiyar Muryar Talaka ta Jihar Katsina ta yi bikin rantsar da shugabannin kungiyar na kananan hukumomi 34 da ke…

A ranar Lahadin da ta gabata ce Kungiyar Muryar Talaka ta Jihar Katsina ta yi bikin rantsar da shugabannin kungiyar na kananan hukumomi 34 da ke jihar.

Rantsarwar wadda aka yi a dakin taro na Cibiyar Koyar da Sana’o’i, ta Katsina ta gudana ce a karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar ta Jihar Alhaji Sanin Shaga Kofar Kaura.

Shugaban Kungiyar ta Jihar ya ce, wannan rantsarwa na daya daga cikin alkawurran da suka dauka a lokacin da aka zabe su don ganin cewa sai an samu shugabancin wannan kungiyar a dukan kananan hukumomin jihar domin tafiyar da harkokin kungiyar a yankunansu.

Shugaban ya yi kira gare su da su zama tsintsiya madaurinki daya, “Kada ku bari a shigo a raba kawunanku walau ta fuskar yaudara ko romon baka da sunan za a yi muku wani abu. Ku sani yanzu lokaci ne na siyasa, to ku fitar da kungiya daga shiga rikicin siyasa. Kowa ya bi ra’ayinsa. Sannan ofishina a bude yake gare ku a kowane lokaci domin sauraren duk wani abin da za ku zo da shi,” inji shi.

Babban Bako kuma Shugaban Riko na Kasa na Kungiyar Alhaji Musbahu Daura Dole nuna farin cikinsa ya yi a kan wannan ci gaba da sauran nasarorin da kungiyar take ta samu a fadin kasar nan duk kuwa da tarnakin da take samu da wadansu marasa son ci gaban kungiyar ke jawowa.

Kazalika, ya ja hankalin shugabannin a kan su san cewa, “Ku sani kamar yadda kuka san wannan kungiya ta Muryar Talaka, to duk abin da za mu yi za mu yi shi ne da sunan talakan ba don biyan wata bukata ta kashin kanmu ba. Muna wakiltar talakan ne musamman wanda ga shi da abin magana amma bai san yadda zai yi ba. Kila yana da wani koke ko shawara ga gwamnati ko kuma wadanda abin ya shafa amma bai san ta inda zai mika ba, to mu ne wakillansa. Don haka ya zama wajibi mu bi duk wata hanya domin ganin cewa lallai Muryar Talakan ce ba ta Musbahu ko Sanin Shaga ba,” inji Daura Dole.

Shugabanni sun yi rantsuwar kama aiki ne bisa jagorancin Barista Sani Yahaya Wurna wanda kuma shi ne Sakataren Kungiyar Lauyoyi ta Jihar Katsina.