Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi ya amince da rage lokutan aiki a jihar da sa’o’i biyu ga ma’aikatan gwamnatin jihar a cikin watan Ramadan.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Muhammad K Dagaceri.
- SSANU da NASU za su shiga yajin aikin gargadi
- Ban mayar da hankali kan ɗora wa gwamnatin da ta shuɗe laifi ba —Tinubu
Sanarwar ta ce a yanzu ma’aikatan za su fara aiki da ƙarfe 9 na safe sannan su tashi da ƙarfe 3 na rana daga ranar Litinin zuwa Alhamis sabanin ƙarfe 5 na Yamma da aka saba tashi daga aiki.
A ranar Juma’a kuma, ma’aikata za su fara da ƙarfe 9 na safe sannan su tashi da ƙarfe 1 na rana kamar yadda aka tsara.
Sanarwar ta kuma ce an ɗauki matakin ne domin bai wa ma’aikatan gwamnati isasshen lokaci da damar haɓaka ayyukan ibada a cikin wannan wata mai alfarma.
Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa, “ana fatan ma’aikatan jihar za su yi amfani da lokacin azumin watan Ramadan wajen yi wa jihar addu’ar zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin jihar da ma Najeriya baki daya.”