✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An rage farashin Data da kashi 50 a 2020 a Najeriya

NCC ta ce an rage farashin 1GB na data zuwa N487.17 a Najeriya

Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce an dauki matakan rage farashin data da kusan rabi a shekarar 2020.

NNC ta ce Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya bayar da umarnin yin hakan daga 2020 zuwa 2025 bayan kafa kwamitin kasa na samar da hanyoyin sadarwa a 2021.

Hadimin ministan kan fasahar sadarwar zamani, Femi Adeluyi ya ce farashin 1GB na data ya koma N487.17 daga N1,000 daga watan Janairu zuwa Nuwamban 2020.

“Manufar hakan ita ce rage farashin 1GB na data ya koma N390 a shekarar 2025.

“Bayan sa N1,000 a matsayin farashi mafi tsada na 1GB, ana sa ran zai rika raguwa a karshen kowace shekara N925 a 2020: N850 (2021); N772 (2022); 700 (2023); N545 (2024); da N390 (2025)”.

Adeluyi ya ce sabanin farashin N925 da aka tsara zuwa karshen 2020, farashin ya ragu zuwa N487.18, kuwan rabi (kashi 47.33) na farashin.

Da take kira ga masu korafi su gabatar da shi gare ta, NCC ta ce ta dauki matakan tabbatar da kyakkyawan farashi da kuma ganin kamfanonin sadarwa ba sa tsawwala wa jama’a.

 

Ba mu gani a kasa ba, inji masu amfani da data

Sai dai masu amfani da data da Aminiya ta zanta da su sun musanta ikirarain gwamantin; A cewarsu har yanzu ba ta sauya zani ba domin a kan N1,000 suke sayen 1GB na data.

Daga cikinsu, Mukhtar Abdullahi mazaunin Sabon Gari, Kano, ya ce bai ga wata alamar cewa an rage farashin data ba.

“Ba gaskiya ba ne, watakila kamfanonin sadarwan ne ba su rungumin tsarin ba; ko da safen nan sai da na sayi 1GB a kan N1,000’’, inji wani mai suna Deji Eluobomi.

Wani mazaunin Legas, Muyiwa Ayinde Kareem, ya yi fatali da ikirarin na NCC da cewa: “Ba a rage sisi ba. Ni ya kamata in fi kowa sani idan an samu ragi saboda ni kasuwancin data nake yi’’.

Idan za a iya tunawa a watan Nuwamban 2019 ne Pantami ya umarci hukumar ta yi zama da kamfanonin sadarwa a kan yadda za a rage tsadar data a Najeriya.

Bayan zaman kungiyar masu harkar (ALTON) ta ce akwai kama-karya a umarnin na gwamnati wanda suka ce ka iya karya gwiwar masu zuba jari a bangaren su shigo kasar.