Gwamnatin Jihar Kano ta amince da ƙunshin sabbin shugabannin da za su jagoranci gudanarwar Ƙungiyar Wasan Ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars.
Wannan kuwa ya biyo bayan ƙarewar wa’adi da kuma saukar da tsofaffin shugabannin ƙungiyar suka yi a watannin baya.
- Man United za ta gina sabon filin da zai ɗauki ‘yan kallo 100,000
- A ba INEC damar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi — IPAC
Bayanin hakan na ƙunshe a cikin takardar da mai magana da yawun Gwamnan na Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu.
A cewar takardar shugabannin waɗanda aka bi cancanta wajen zaƙulo su za su ja ragamar ƙungiyar ne na tsawon shekara ɗaya wanda akwai yiyuwar ƙarin wa’adin shugabancinsu idan har sun yi aiki mai kyau.
Sabbin shugabannin sun haɗa da Ali Muhammad Umar (Nayara Mai Samba) — a matsayin Shugaba.
Sai Salisu Kosawa — a matsayin mamba da Yusuf Danladi (Andy Cole) da Nasiru Bello da Muhammad Ibrahim (Hassan West) — da Muhammad Usman da Muhammad Danjuma Gwarzo da Mustapha Usman Darma da Umar Dankura da Ahmad Musbahu da Rabiu Abdullahi da Abubakar Isah Dandago da Injiniya Usman Kofar Naisa a matsayin membobin ƙungiyar.
Haka kuma Yamalash zai zama Daraktan watsa labarai na ƙungiyar da kuma Ismail Abba Tangalash a matsayin mataimakinsa.
Har ila yau Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana gamsuwarsa akan jagorancin sabbin shugabannin inda ya bayyana cewa shugabancinsu zai samar da ci gaba ga ƙungiyar ta Kano Pillars.
Ya ce ana sa rai shugabannin za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Ma’aikatar Matasa da Wasanni da sauran masu ruwa da tsaki a Jihar don ciyar da ƙungiyar gaba.
Haka kuma Gwamnatin da naɗin Kaftin din Ƙungiyar Wasan Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa Super Eagles Ahmed Musa a matsayin ambasadan Harkokin Wasanni na Jihar Kano da nufin zaburarwa ga ’yan wasan da kuma ƙara wa ƙungiyar ta Pillars farin jini da kuma karɓuwa a wajen jamaa.
Jerin shugabannin Kano Pillars
Aliyu Nayara Mai Samba — Shugaba
Salisu Muhammad Kosawa — Mamba
Abubakar Isa Ɗandago — Jami’in watsa labarai
Ismail Abba Tangalash —Mataimakin Jami’in watsa labarai
Yusuf Danladi Andy Cole — Mamba
Muhammad Usman — Mamba
Ahmad Musbahu — Mamba
Umar Umar Dankura — Mamba
Rabiu Abdullahi — Mamba
Nasiru Bello — Mamba
Muhammad Danjuma Gwarzo — Mamba
Mustapha Usman Darma — Mamba
Muhammad Ibrahim (Hassan West) — mamba
Injiniya Usman K/Naisa — Mamba