Dokta Sa’idu Wanzam, matashin wanzami ne dan asalin Jihar Katsina da aka haife shi a garin Maiduguri kimanin shekara 40 da suka wuce kuma ya shahara wajen aikin wanzanci da ba da maganin gargajiya.
Wanzamin wanda yake da asibitin gargajiya a garin Jos, shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Masu Maganin Gargajiya ta Jihar Gombe kuma Sakataren Labarai na Kungiyar Wanzamai ta Kasa a Shiyyar Arewa maso Gabas.
Kwarewarsa da kokkarinsa a sana’ar wanzanci gami da cancantarsa suka sa a makon jiya Hakimin Bogo a Jihar Gombe Alhaji Baddi Galadima, ya nada shi Sarkin Askan Hakimin Bogo.
Kafin nada Sa’idu Wanzam, shi ne Sarkin Askar Dagacin Bogo, Malam Dahiru Waziri, yanzu kuma ya zama Sarkin Askar Hakimin Bogo, kuma shi ne shugaban Matasan Wanzamai na Jihar Gombe, sannan Sintalin Sarkin Askar Gombe Alhaji Sani Sambo.
Bayan nadin nasa Hakimin Bogo Alhaji Baddi Galadima, ya gode wa ’yan uwa da suka halaraci yi wa Dokta Sa’idu Wanzam nadin Sarkin Askar.
Alhaji Baddi Galadima, ya yi fatan wannan zumuncin na wanzamai zai dore domin suna yi wa junan su kara a duk lokacin da wani hidima tasu ta taso.
Hakimin ya jinjina wa Sarkin Askar Gombe Alhaji Sani Sambo, kan yadda ya hada kan wanzamai a karkashinsa suke biyayya ga juna inda ya ce, biyayyar ce kawai tasa aka yi masa rawani a matsayin Sarkin Askar Hakimi.
Da yake jawabin godiya bayan nadin Dokta Sa’idu Wanzam, cewa ya yi ya ji dadi da farin ciki kan wannan nadi da Hakimi ya yi masa domin abin alfahari ne gare shi.
Sa’idu Wanzam, ya yi kira ga wanzamai cewa, su tsaya sosai wajen kare martabar sana’arsu ta wanzanci domin ba aski ne kadai sana’ar wanzami ba akwai cire hakkin wuya da makamantan aikin jini irin nasu na gado.
Bayan nadin a gidan Hakimin Bogo a Unguwar Bolari Gadar Malale a Gombe an wuce zuwa sabon gidan Dokta Sa’idu Wanzam da ya tare da ke Unguwar Hayin Kwarin Misau, inda Wanzamai suka yi wasanninsu na gargajiya.
Maharba da ’yan tauri sun taya wanzaman murna wajen halartar taron su kuma nuna irin tasu bajintar.