Majalisar Gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS), ta sanar da nadin Farfesa Mu’azu Abubakar Gusau a matsayin sabon Shugaban jami’ar.
Sanarwar ta fito ne daga bakin Shugaban Majalisar, Honarabul Yissa Ezekiel Benjamin a babban dakin taro na jami’ar bayan zaman majalisar na musamman karo na 20 da aka gudanar a ranar Alhamis, 10 ga watan Dasumba.
- An ceto dalibai 200 bayan harin ’yan bindiga a GSSS Kankara
- Mai gidan jaridar Leadership, Sam Nda-Isaiah ya rasu
Honarabul Yissa ya bayyana cewa tsarin zabar sabon shugaban jami’ar ya fara ne tun yayin da Jami’ar ta ta tallata bukatar hakan a wasu manyan jaridu biyu na kasar.
Ya ce Farfesa Mu’azu ya zama gwarzo daga cikin bajiman malamai 25 daga jami’o’i daban-daban da suke nemi shugabancin jami’ar bayan cika ka’idodin da aka shar’anta.
Farfesa Mu’azu wanda shi ne cikon Shugaban jami’ar na uku a tarihi, zai yi aiki na wa’adin shekaru biyar a karon farko wanda zai fara daga ranar 10 ga watan Fabrairun 2021.
Aminiya ta ruwaito cewa Farfesa Mu’azu wanda ya fito daga jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato, kwararre ne a fannin nazarin yanayi da tasirin sunadarai a jikin halittu wato Toxicology kuma ya yi karatun digirin digirgir a Jami’ar Surrey da ke Birtaniya.