✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kubutar da masu ciki a gidan kyankyasar jarirai

Rundunar ’Yan Sanda Jihar Kuros Ribas ta kubutar da wasu mata uku masu ciki da kananan yara biyu a gidan safarar jarirai da ke kauyen Obot…

Rundunar Yan Sanda Jihar Kuros Ribas ta kubutar da wasu mata uku masu ciki da kananan yara biyu a gidan safarar jarirai da ke kauyen Obot Udonna na Karamar Hukumar Akamkpa.

Kwamishinan ’Yan sandan jihar, Abdulkadir Jimoh, ya ce sun kubutar da matan ne ranar Laraba, sakamakon bayanan sirri da suka samu.

Ya ce matar da ake zargin ta amsa laifinta ta kuma ce ta sayar da jarirai uku, kowacce a kan Naira 500,000.

Ya ce sun kuma gano wata mata da suke yin harkar tare, wadda ke zaune a Technical Junction, na birnin Kalaba.

“Suna nan tsare a wurinmu, kuma ana cigaba da bincike,” kamar yadda takardar da ya fitar ta.