✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An koro Rivers United daga CAF Confederation Cup

Kungiyar Young Africans za ta fafata da Gallants ta Afirka ta Kudu.

Kungiyar Young Africans ta Tanzania ta fitar da zakarun Najeriya, ’yan kungiyar Rivers United daga gasar CAF Confederation Cup.

‘Yan wasan na tawagar su Stanley Eguma sun tashi babu da babu, wato 0-0 da masu masaukinsu a filin wasa na Benjamin Nkapa da ke Dar es Salam da daren ranar Lahadi.

’Yan Young Africans sun yi nasara a wasan daf da na kusa da karshe da ci 2-0.

An dakatar da wasan bayan an shafe mintuna 24 ana wasan saboda matsalar fitilar filin.

An bai wa kungiyoyin biyu minti 10 su motsa jiki kafin a sake fara wasan.

‘Yan wasan Rivers United sun yi kokari matuka amma sun kasa kutsawa cikin gidan masu masaukin bakin.

Kungiyar Young Africans za ta fafata da Gallants ta Afirka ta Kudu a wasan kusa da na karshe.