✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kori duk ministoci kan zargin cin hanci da rashawa a Malawi

Za a kafa wata sabuwar majalisar ministocin cikin kwana biyu.

Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera ya kori gaba daya ministocinsa bisa zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa galibinsu.

A wani jawabi da ya yi ga al’ummar kasar ta talabijin a ranar Litinin, shugaban ya lashi takobin tunkarar duk wata matsalar kin bin doka daga jami’an gwamnati.

Ya ce za a kafa wata sabuwar majalisar ministocin cikin kwana biyu.

Bayanai sun ce a bayan nan an zargi ministocinsa uku da laifukan da suka shafi almundahana da cin hanci da rashawa, wanda shugaba Lazarus Chakwera ya ba da goyon bayan sai sun fuskanci tuhumar da ake yi musu.

Daga cikin ministocin da wannan lamari ya shafa, akwai Ministan Kula da Harkokin Filaye, wanda aka kama a watan da ya gabata a kan zargin cin hanci.

Shi kuwa Ministan Kwadago ana zarginsa ne da karkatar da kudin yaki da annobar Coronavirus, yayin da Ministan Makamashi ke fuskantar zargin almundahana a kwangilolin mai.

Dukkaninsu sun musanta zargin kamar yadda BBC ya ruwaito

An zabi Mista Chakwera a shekarar 2020, inda ya yi alkawarin yakar cin hanci da rashawa.

A makon da yan gabata e wasu kungiyoyin coci biyu masu karfin fadi a ji suka zargi shugaban da cewa ba ya kokari wajen yaki da matsalar cin hanci.