Uganda ta kawo karshen annobar cutar Ebola bayan wata hudu da fara bullarta a kasar.
A ranar Laraba gwamnatin kasar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka ayyana karshen annobar, wadda ta kashe mutum 55 a kasar.
- Almundahanar N96bn: Wike ya sake maka Amaechi a kotu
- HOTUNA: Masaukin Ronaldo da budurwarsa a Saudiyya
“Mun yi nasarar kawo karshen annobar Ebola,” in ji Ministar Lafiya ta Uganda, Jane Ruth Aceng, a lokacin bikin kawo karshen annobar a Mubende, yankin da aka fara gano kwayar cutar a watan Satumbar 2022.
A kwana 113 da aka yi fama da ita, mutum 142 sun harbu a annobar, daga cikinsu 55 sun rasu, wasu 87 kuma sun warke.
WHO kan ayyana karshen annobar Ebola ce idan aka samu kwana 42 a jere ba tare da kara samun bullar cutar ba.
WHO ta ambato ministar lafiyar Uganda na cewa, “Mun dauki matakan gaggawa,” da suka dace domin murkushe annobar.
WHO ta danganta annobar ta Uganda da kwayar Sudan Ebola virus, wadda kawo yanzu ba a samu rigakafinta ba.