✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe yarinya bayan garkuwa da ita a Kano

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta gano gawar wata yarinya mai kimanin shekara 8 da aka yi garkuwa da ita a wata rijiya a Unguwar…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta gano gawar wata yarinya mai kimanin shekara 8 da aka yi garkuwa da ita a wata rijiya a Unguwar Gandun Albasa a Karamar Hukumar Birni da Kewaye.

Kakakin Rundunar DSP Haruna Abdllahi Kiyawa ya bayyana cewa an yi garkuwa da marigayiyar ce a Unguwar Tudun Wada a Karamar Hukumar Nasarawa.

DSP Haruna Kiyawa ya ce wadansu mutane ne suka sanar da rundunarsu cewa an tsinci gawa a cikin wata rijiya lamarin da ya sa jami’ansu suka yi kokarin fito da gawar inda aka gaggauata kai ta a Asibitin Kwararru na Murtala “Daga baya ne aka gano cewa gawar ta wata yarinya ce mai suna A’isha Umar wacce aka yi garkuwa da ita a Unguwar Tudun Wada a makon jiya,” inji shi.

Sai dai DSP Kiyawa ya ce tuni rundunar ta kama wadansu mutane da ake zargi  da hannu a garkuwa da yarinyar inda rundunar ta bazama neman manyan da ake zargi da garkuwa da  marigayiyar.

“Jami’anmu da ke aiki a Sashen Yaki da Garkuwa da Mutane da  na Ofishin Puff Adder ne suka kama wadanda ake zargi da garkuwa da yarinyar,” inji Kiyawa.

Ya ce tuni Kwamshinan ’Yan sandan Jihar Kano CP Ahmed Iliyasu ya bayar da umarnin a kamo sauran wadanda ake zargin da suka tsere. Ya kuma ce da zarar an kamamla bincike za a gurfanar da wadanda ake zargi gaban kotu.                                                                                                                                              DSP Kiyawa ya yi kira ga al’ummar jihar su rika sanar da rundunar kan duk wani abu da ya faru a unguwanninsu ko wadansu da ba su amince da ayyukansu ba don daukar matakin da ya dace cikin gaggawa tare da gurfanar da masu laifin gaban kotu.

Aminiya ta gano cewa a makon jiya ne aka yi garkuwa da marigayiya A’isha a lokacin da ta taso ita da ’yan uwanta daga Makarantar Islamiyya inda aka ce wata mata sanye da nikabi ta yi awon gaba da ita.

Daga baya ne kuma wadanda suka yi garkuwa da marigayiyar suka nemi a biya kudin fansa Naira miliyan shida inda suka nemi a ba mahaifiyarta kudin a cewarsu ita suke so ta kai musu kudin ba namiji ba.

Sai dai ganin cewa an dauki kwanaki ba a biya kudin ba, ake zaton hakan ya janyo suka kashe yarinyar suka jefa ta a cikin rijiya.