✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe matashi yayin rikici a ƙauyukan Kano

Rahotanni sun nuna cewar an farmaki matashin ne lokacin da yake hanyar komawa ƙauyensu.

Rikici ya ɓarke tsakanin wasu matasa a ƙauyukan Faruruwa da Tarandai da ke Ƙaramar Hukumar Takai a Jihar Kano, inda aka kashe wani matashin har lahira.

Rikicin ya faru ne a ranar cin kasuwa kuma ya rikiɗe zuwa tashin hankali, inda aka ƙone rumfunan kasuwar.

Wani masani kan harkar tsaro, Zagazola Makama ne, ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Lahadi.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:45 na daren ranar 23 ga watan Mayu, 2025, a kasuwar Faruruwa.

A cewarsa, rikicin ya samo asali ne bayan wani matashi mai shekaru 28, Sani Yunusa daga ƙauyen Toho Diribo ya ziyarci budurwarsa a Tarandai.

Yayin da yake komawa gida, wasu matasa suka kai masa hari da sanda da adda.

Jami’an tsaro sun isa wajen cikin gaggawa don daƙile rikicin da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Rundunar ’yan sandan jihar, ta fara bincike don gano musabbabin rikicin da kuma kama waɗanda suke da hannu a kisan matashin.