Mahara sun bindige wani sannanen dillalin shanu a Sabon Garin Tabkin Kazai da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara saboda kin amincewarsa ya siyan shanun da aka sato.
Mazauna sun shaida wa Aminiya cewa, ’yan bindigar da suka yi wa garin shigar bazata, kai tsaye suka nufi wurin dillalin shanun mai suna Alhaji Audu Mai Sayen Shanu, wanda aka fi sani da Audu na ’Yar yaye kuma suka harbe shi nan take sannan suka arce.
- ’Yan ta’adda 15 sun shiga hannu a Legas
- Coronavirus ta kashe karin mutum 3 a Najeriya, 749 sun harbu
Sun ce, “Alhaji Audu ya shahara sosai a Gabashin Karamar Hukumar Tsafe kuma a hakikanin gaskiya ba ya da na daya a wajen sayen shanu.
“A baya kusan sau uku mahara dauke da makamai ke shigowa garinmu su yi awon gaba da dabbobi.
“Sau da yawa sun saba kawo masa shanun sata amma sai ya ki amincewa tare da yin watsi da bukatarsu ta neman kulla wata alaka ta kasuwanci da su.”
“Ya rika shaida masu cewa tun da dadewa ya daina harkar shanu bayan ya fahimci cewa shanun sata sun mamaye kasuwanni da dama a wannan shekara.
“Bayan da suka kashe shi sun kama gabansu ba tare da karbar ko sule a hannunsa ba kuma galibin mazauna garin ba su da masaniyar an kashe shi saboda shi kadai suka yi wa takakkiya,” a cewa wani mazauni.
Ya zuwa tattara wannan rahoto, babu wani bayani da ya fito daga Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Zamfara dangane da lamarin kuma duk wani kokari da Aminiya ta yi na tuntubar kakakin rundunar, SP Muhammad Shehu, ya ci tura.