✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama Shugaban YLAN a matsayin matashin da ya fi gwagwarmaya

An karrama Shugaban YLAN, reshen Jihar Kaduna, Kwamrade AY Babanyara a matsayin matashin day a fi kowa gwagwarmaya a Jihar Kaduna. Croccity award ne ta…

An karrama Shugaban YLAN, reshen Jihar Kaduna, Kwamrade AY Babanyara a matsayin matashin day a fi kowa gwagwarmaya a Jihar Kaduna.

Croccity award ne ta bayar da wannan lambar girman ga shugaban na YLAN, bayan an gabatar da zabe, inda ya samu damar zama wanda ya fi kowa gwagwarmaya bayan ya samu kashi 74.36 cikin dari na kuri’un da aka kada.

Da yake jawabi bayan ya samun wannan karramawa ta musamman, Kwamrade Banayara ya nuna farin ciki bisa yadda ya samu wannan lambar yabo, inda yake cewa “Ina matukar dogiya ga Allah madaukakin sarki da ya nuna min wannan rana da nake karban wannan lambar yabo a matsayin matashi da ya fi gwagwarmaya a Jihar Kaduna. Wannan ba karamin abun farin ciki bane.

“Sannan kuma in godiya da abokanan gwagwarmaya a duk fadin Najeriya da ke tare da ni komai wuya, komai dadi, musamman a lokacin da ake zaben wanda ya fi gwagwarmayar na ban. Na gode, Allah Ya bar zumunci. Yanzu aka fara gwagwarmaya,” inji Babanyara.