✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama daliban da suka yi nasara a gasar makarantun sakandaren Jihar Legas

Daliban makarantun sakadaren Jihar Legas da suka yi nasara a gasar wasannin  shekarar 2015 ta makarantun sakandaren jihar wacce ake yi wa lakabi da IBILE…

Daliban makarantun sakadaren Jihar Legas da suka yi nasara a gasar wasannin  shekarar 2015 ta makarantun sakandaren jihar wacce ake yi wa lakabi da IBILE Games sun samu kyaututtuka na musamman daga gwamnan Jihar Babatunde Raji Fashola.
An gudanar da bayar da kyaututtukan wanda aka yi musu lakabi da kyautar  Adidas ta musamman a filin wasa na Teslim Balogun da ke Jihar Legas a karshen makon da ya gabata.
dan shekaru 16 da haihuwa mai suna Yinusa Idowu dan aji uku a karamar makarantar sakandare ta Mobolaji Bank Anthony da ke unguwar Yaba ya samu kyautar zinare biyar a rukunin motsa jiki na yara maza sai ’yar shekaru 13 da haihuwa mai suna Morayo Okungbuwa ’yar aji uku a karamar makarantar sakandare ta Meadow Hall da ke unguwar Lekki ta samu kyautar gwala-gwalai takwas da azurfa biyu a wasan ninkaya a bangaren mata.
Shi kuwa Oluwadare Samuel dan kimanin shekaru 15 dan aji 2 a Kwalejin kuestland da ke yankin Idimu ya samu kyautar gwal-gwalai uku a wasan dara na bangaren maza, sai Ojo Benson ’yar shekaru 15 da haihuwa da ke aji 2 na makarantar sakandare ta Ipakodo Senior Grammar School ta lashe kyautar gwalagwalai bakwai da kuma azurfa daya a wasan ninkaya na bangaren mata.
Hakazalika an karrama makarantun nakasassu da suka shiga gasar kamar makarantar nakasassu ta Wesley School 1 ta kurame da ke yankin Surulere ta lashe kyautar yara maza da suka fi nuna gwaninta, ita ma karamar makarantar sakandare da ke yankin Surulere ta lashe kyautar mata da suka fi nuna gwaninta.
Kwalejin Do-Estdot da ke unguwar Idimu ta lashe kyautar yara maza da suka nuna kwarewa, sai makarantar sakandare ta Surulere ta sami kyautar yara mata da suka fi nuna kwarewa.
An karramar dalibai biyu daga kowane bangare na motsa jiki da suka shiga gasar wadanda suka nuna kwarewa ta musamman a gasar.
Da yake jawabi a wurin bikin bayar da kyaututtukan, gwamnan jihar Babatunde Raji Fashola ya bukaci daliban su mayar da hankali wajen karatunsu tare da tabbatar da ganin sun cimma burin da suka sanya a gaba na wasannin motsa jiki.
Gwamnan ya yaba wa wadanda suka shirya gasar saboda kokarin da suka nuna wajen bunkasa harkokin wasanni a jihar.