✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kammala gasar Polo ta Katsina

A ranar Asabar da ta gabata ne aka kammala gasar kwallon dawaki (Polo) a Katsina na shekara ta 2016 wanda kuma yake mabudin cigaba da…

A ranar Asabar da ta gabata ne aka kammala gasar kwallon dawaki (Polo) a Katsina na shekara ta 2016 wanda kuma yake mabudin cigaba da wannan gasa a wannan shekara a sauran wuraren da ake gudanar da ita a fadn kasar nan.
 ‘Yan wasan da suka fito daga Kano su ne suka shigo da kafar dama a wannan gasa ta wannan shekara, domin sun koma gida da kofuna biyar.
Tawagar ‘yan wasan Kano Titan su ne suka lashe babban kofin wannan gasa wato kofin Najeriya, a inda suka lallasa abokan karawarsu na tawagar ‘yan wasan Mad Air. A cikin gumurzun da suka yi don cin wannan kofi, Kano Titan ta doke Mad Air da kwallaye 8 da 4. Har’ ila yau, tawagar ‘yan wasan Polon da suka fito daga Kanon, wato Kano Bagauda su ne suka lashe kofi na biyu na Janar Hassan a inda suka kwashe kwallaye 7 suka bar Bauchi Dokaji da kwallaye 3.
Shi ma kofin Shugaban kasa, Kano Susplan ne suka lashe daga abokan kararwarsu na Katsina Air Peace da kwallaye 7 a kan 6. Kofin Gwamna ma ‘yan wasan na Kano Bagauda ba su bar shi a baya ba, domin su suka lashe shi da kwallaye 7 a kan Bauchi Dokaji mai kwallaye 3. Sai kofin Sarkin Katsina Abdulmuminu Kabir Usman wanda shi ma Kano Nakudu suka lashe shi a karawar da suka yi da ‘yan wasan Zariya Zar Project.
Kaduna Dattaku ita ce ta yi nasara akan Kano Susplan a gasar cin kofin Talba, yayin da Katsina Eber Green Farm ta yi nasara a kan Zariya Zar a kofin Commasie.  Kazalika, ‘yan wasan Katsina Eber Green Farm su suka lashe kofin tunawa da Sarkin Katsina Muhammadu Kabir Usman Nagogo a kan abokan karawarsu na Fatakwal Shabbazz.
A kofin tunawa da Sarki Usman Nagogo an fafata ne a tsakanin tsofaffinf ‘yan wasan na Polo da kungiyar ‘yan wasan Polon na jami’an ‘yan sanda na kasa, tsofaffin ’yan wasan ne suka yi nasara. Shi ma kofin Shugaban kungiyar wasan Polon na dindindin, kuma tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Alhaji Muhammadu Lawal Kaita ba a bar shi a baya ba. Shi dai wannan kofin ana sanya gasarsa ne a tsakanin matasa masu koyon wasan polo na ‘yan kasa da shekaru 16 inda ake raba su a tsakanin tawagar (A) da (B). To ‘yan wasan (B) su suka yi nasara.
 Tun daga ranar da aka fara wasan har aka gama, babu wani rahoto da aka samu na aukuwar hadari. An fara lafiya an kuma gama lafiya cikin kyakkyawan yanayi da kuma matakan tsaro. Sai dai a bisa al’adar wannan wasa, ba kasafai ake yin wani jawabi ba a wajen bude shi ko rufewa, sai dai ana bayar da kyaututtuka ga ‘yan wasan da suka nuna wata bajinta ba ya ga kofunan da aka lashe.