✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wanda ake zargi da kashe Fahim Saleh

Tyrese Haspil ya sace wa mai gidansa kudi Dala 100,000 amma Fahim Saleh bai kai kararsa ba.

‘Yan sandan sun tsare mataimaki na musamman ga matashin dan kasuwa Fahim Saleh, wanda aka yi wa kisan gilla a makon jiya.

Ana zargin mataimaki na musamman ga hamshakin dan kasuwar, Tyrese Devon Haspil, mai shekaru 21 da hannu a kisan mai gidansa.

‘Yan sanda a birnin New York na kasar Amurka sun kama wanda ake zargin ne a ranar Juma’a kwana biyar da kashe Fahim Saleh.

Ana zargin Tyrese Haspil ya sace wa mai gidansa zunzurutun kudi Dalar Amurka 100,000 amma Fahim Saleh bai kai kararsa ga ‘yan sanda ba, sai suka shirya tsarin da zai bi ya biya shi kudin a hankali, amma ya saba tsarin.

‘Yar uwar mamacin ta fara gano gawarsa bayan kimanin sa’a 24 da kashe shi, a lokacin da ta je gidan domin ta duba shi saboda ba ta ji duriyarsa ba.

Mahukunta a birnin na New York na zargin an yi hayar makashin Fahim ne, kana mutuwarsa na da alaka da harkar kudi da ya kulla da wasu abokan kasuwancinsa.