✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum biyu kan zargin fashi da makami a Jigawa

A halin yanzu dai mutum biyu na kauyen Masama da ake zargi da laifin sun shiga hannu.

Rundunar ’yan sanda a Jigawa ta samu nasarar cafke wasu mutum biyu da ake zarginsu da ta’adar fashi da makami a Karamar Hukumar Gumel ta Jihar.

ASP Zubairu Aminuddeen, Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai ranar Laraba a Dutse, babban birnin Jihar.

Aminuddeen ya ce, ababen zargin sun shiga hannu ne a ranar 10 ga watan Afrilu, bayan sun shiga gidan wani Malam Haruna Mohammed a kauyen Masama inda suka far wa dansa mai shekaru 35.

Kakakin rundunar ’yan sandan ya yi zargin cewa, mutanen da ake zargi sun harbi dan Malam Haruna da wata bindiga kirar gida sannan suka sassare shi da adda, lamarin da ya gadar masa da raunuka daban-daban.

Ya ci gaba da cewa, ababen zargin sun kuma yi awon gaba da Naira miliyan daya yayin da suka kai harin.

A cewarsa, bayan samun rahoton aukuwar lamarin ne suka tura tawagar jami’an ’yan sanda zuwa gidan inda suka mika wanda lamarin ya shafa zuwa Babban Asibitin Gumel.

“A halin yanzu dai mutum biyu da suka fito daga kauyen Masama wadanda ake zargi da laifin sun shiga hannunmu,” a cewar sa.

ASP Aminuddeen ya ce za su ci gaba da zurafafa bincike domin gurfanar da ababen zargin a gaban Kuliya.