✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama motocin fasakwauri da alamomin UNICEF da NNPC a Kaduna

Hukumar Kwastam a Jihar Kaduna ta yi nasarar kama wasu motoci 39 wadanda aka shigo da su ta barauniyar hanya masu dauke da tambarin Hukumar…

Hukumar Kwastam a Jihar Kaduna ta yi nasarar kama wasu motoci 39 wadanda aka shigo da su ta barauniyar hanya masu dauke da tambarin Hukumar UNICEF da na NNPC.

Mataimakin Kwanturolan Kwastam, DCC Baba Kura Kolobe ne ya sanar da haka lokacin da yake nuna motocin da sauran kayayyaki da suka kama ga manema labarai a Kaduna.

Ya ce ma’aikatansu sun kuma  kama buhun shinkafa 5,600 da aka shigo da su.

“Mun kuma kama kayan gwanjo har dubu 1,953 da man gyada jarka lita 25 guda 1,095. Sai motoci 39 ciki har da wadanda ke dauke da tambarin UNICEF da NNPC sai kuma wasu motoci ’yan Kwatano da muka kama a bakin iyakokin kasar nan,” inji shi.

Ya shawarci jama’a musamman ’yan kasuwa su rika bin ka’ida wajen shigo da kayayyaki kasar nan inda ya ce yin hakan zai taimaka wa tattalin arzikin kasa.

“Muna kare rayukan ’yan kasa ne domin yawancin kayayyakin da ake shigowa da su musamman shinkafa da gwanjo na da hadari ga rayukan jama’a da kuma tattalin arzikin kasar nan. Domin ba muna kama mutane ba ne domin kawai mu cutar da su, manufarmu ita ce mu kare kasar nan kuma mu bunkasa tattalin arzikinmu wanda hakan ya sa dole mu hana shigo da kayayyakin da gwamnati ta haramta shigo da su domin bai wa na gida damar bunkasa,” inji shi.