✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matsafa da busassun gawarwaki 20 a Edo

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Edo ta kama wasu mutum uku a wani dakin tsafi dauke da tsofaffin gawarwaki 20 da aka busar. Rundunar ta bayyana…

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Edo ta kama wasu mutum uku a wani dakin tsafi dauke da tsofaffin gawarwaki 20 da aka busar.

Rundunar ta bayyana hakan ne ranar Alhamis a Benin, babban birnin jihar cikin wata sanarwa da ta fitar ta bakin mataimakin Kakakinta, ASP Jennifer Iwegbu.

Jennifer ta ce an gano gawarwakin ne a wani gida da ke unguwar Asoro da ke birnin na Benin.

Ta ce, “Biyo bayan wasu bayanan sirri da muka samu cewa an gano wasu gawarwaki a unguwar Asoro, mun tura tawagarmu cikin gaggawa unguwar, kuma mun samu nasarar kamo mutane uku a gidan, yayin da sauran suka tsere.

“Baya  ga haka kuma, mun gano gawarwakin maza 15 da su ma aka busar, da na mata uku, sai kuma na kananan yara biyu.

“Ganin haka Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Abutu Yaro, ya ba wa Mataimakinsa na sashin binciken sirri umarnin binciko musabbabin mutuwar gawarwakin,” inji ta.

Jennifer ta kuma ce al’ummar jihar su kwantar da hankalinsu, domin za su cigaba da tabbatar da sun kiyaye rayuka da dukiyoyin su kamar dai yadda doka ta dora musu.