✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matashin da ya yi yunkurin tada bam a coci a Kaduna

Rundunar ‘yan sanda ta kama wani matashi mai suna Nathaniel Samuel da ya yi yunkurin tada bam a wani coci a Unguwar Sabon Tasha da…

Rundunar ‘yan sanda ta kama wani matashi mai suna Nathaniel Samuel da ya yi yunkurin tada bam a wani coci a Unguwar Sabon Tasha da ke karamar hukumar Chukun a jihar Kaduna.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da lamarin inda ya ce tuni sun fara binciken matashin.

Ya ce, an kama matashin ne wanda ke zauna a karamar hukumar Chikun a jihar.

Ya kuma bayyana cewa, an kama matashin ne bayan ya ajiye ledar da bam din ke cike ya kuma nufi ban daki.