✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu garkuwa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ce ta yi nasarar kama wadansu mutum uku da ake zaginsu da yin garkuwa da wata amarya da ’yan…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ce ta yi nasarar kama wadansu mutum uku da ake zaginsu da yin garkuwa da wata amarya da ’yan uwanta uku a kan hanyar Jos kusa da Dajin Falgore lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa bikin amaryar.

An yi garkuwa da amaryar ce wadda aka boye sunanta da sauran ’yan uwanta uku ciki har da angonta wadanda ke cikin motoci biyu inda masu garkuwar suka yi musu fashi daga bisani suka yi garkuwa da su.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi, ya ce jami’an tsaron da suka yi aikin wadanda suka hada da ’yan sanda da sojoji da jami’an farin kaya sun yi gaggawar kai wa mutanen dauki tare da tseratar da su bayan sace su da ’yan mintuna.

DSP Haruna ya ce bayan sun samu kiran gaggawa daga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su tare da sanar musu inda lamarin ya faru, rundunar  ba ta yi kasa a gwiwa ba ta kutsa cikin dajin inda ta yi nasarar tsreratar da mutanen da kuma kama wadanda suka yi garkuwa da su har su 20 a cikin dajin inda kuma wadanda aka yi garkuwa da su din suka gane mutum uku daga cikinsu a matsayin wadanda suka yi garkuwa da su.

Yanzu haka dai masu garkuwa da muaten masu suna Abdulkarim Ardo da Ado Musa wadanda mazauna garin Doguwa ne sai Yunusa Sale daga garin Tudun Wada suna gaban ’yan sanda inda ake gudanar da bincike a kan lamarin.