Rundunar ‘yan sandan Borno ta sanar da kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa da kuma fashi da makami.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso ya fitar, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a wani samame da aka kai ƙauyen Chingowa da ke karamar hukumar Konduga a ranar 25 ga Oktoba, 2024.
- An ayyana N70,000 sabon albashi mafi ƙanƙanta a Jigawa
- Jerin shugabannin Hezbollah da Hamas da Isra’ila ta kashe daga 7 ga Oktoban 2023
A yayin samamen ‘yan sanda sun ƙwato bindiga guda ɗaya, harsashi mai rai, da tsabar kuɗi N2,637,000.
“Bincike na farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin suna da alhakin wasu jerin fashi da makami da yin garkuwa da mutane a ƙananan hukumomin Magumeri da Konduga,” in ji sanarwar ‘yan sandan.
“Suna kuma karbar kuɗaɗe daga kauyuka a da sunan ‘haraji’ a mafi yawan lokaci don cimma buƙatun su.”
Kwamishinan ‘yan sanda, CP Yusufu Mohammed Lawal, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin tare da jaddada aniyar rundunar na yaƙi da miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaron jama’a.
Ya kuma buƙaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa don ɗaukar matakin gaggawa.
Za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kuliya don fuskantar hukuncin da ya dace da su bayan an kammala bincike.