✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

An kama karamin yaro da Turji ke amfani da shi ya kai hari

Karamin yaron ya ce Turji ya koya masa sarrafa bindigogi, kuma da shi aka dana wa mutane tarko a yi garkuwa da su

An kama wani karamin yaro mai shekara 14 wanda jagoran ’yan bindigar Jihar Zamfara, Bello Turji, yake amfani da shi wajen kai wa al’ummomi hari.

Bayan an kama dan aiken na Turji, ya shaida wa jami’an tsaro cewa Turji ya ba shi horo kan yadda ake sarrafa bindigogi iri-iri.

Ya kuma bayyana wa jami’an tsaro cewa Bello Turji yakan yi amfani da wajen dana tarko domin kai wa al’ummomi hare-hare da kuma yin garkuwa da mutane.

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC), ce ta cafke dan aiken na Turji a wani samame da ta kai a Jihar Zmafara.

Kakakin NSCDC a Jihar Zamfara, Ikor Oche, ya ce yaron ya shaida musu cewa yakan yi amfani da raunin matan da gungunsu suka yi garkuwa da su, yana yin lalata da su.