✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama fasto da ya yi karyar an yi garkuwa da shi a Kaduna

Dubun wani Fasto mai suna ‎ James Clement ya cika bayan rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama shi saboda yin karyar an yi garkuwa…

Dubun wani Fasto mai suna ‎ James Clement ya cika bayan rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama shi saboda yin karyar an yi garkuwa da shi, da ya yi.

A cewar rundunar wanda ake zargin tare da abokin hadin bakinsa wani matashi mai suna ‎George Otokpa, sun nemi ‘yan uwan Fasto Clement da su biya diyyar Naira miliyan biyar.

Kakakin rundunar yan sandan Yakubu Sabo, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraban.

Ya ce, dubun wanda ake zargin da abokinsa sun cika ne bayan ‘yan uwansa biyu sun kai kara ofishin ‘yan sanda inda daga bisani aka bi sahu har aka yi nasarar gano inda faston ya boye kansa da sunan an yi garkuwa da shi.