✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai samame wajen kula da yara na Malam Niga a Kaduna

Rundunar ’Yan Sandan jihar Kaduna ta kai samame gidan horon yara na Malam Niga da ke a garin Rigasa a jihar Kaduna inda suka kwashe…

Rundunar ’Yan Sandan jihar Kaduna ta kai samame gidan horon yara na Malam Niga da ke a garin Rigasa a jihar Kaduna inda suka kwashe matasa 147.

Aminiya ta fahimci cewa, rundunar ‘yan sandan ta kai samamen ne da safiyar asubahin yau Asabar.

Gwamnar jihar Kaduna Nasir El-Rufai, na wajen a lokacin da aka kai samamen inda aka kwashe matasan zuwa sansanin Alhazai da ke Mando Kaduna.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Yakubu Sabo, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce, gwamna Nasir El-Rufai tare da ‘Yan Sanda ne suka kai ziyarar bazata wannan gida har suka tarar da wasu daga cikin matasan ajiye cikin mari‎.

” Eh, an samu matasan ne a cikin Mari sannan kuma wasu daga cikinsu har su bakwai sun yi zargin cewa, wasu daga cikin matasan na barbararsu. Yanzu haka malamin su na hannun ‘yan sanda yana amsa tambayoyi duk da ya ce, yana da lasisinsa,” in ji shi.

Itama Kwamishinan Kula da jin dadin al’umma Hafsat Baba ta bayyana cewa, akwai mata 22 da baki ‘yan kasar Nijar biyu da Kamaru biyu da aka samu a cikin gidan Horon matasan.

Ta bayyana cewa, a yanzu ma’aikatan ta na daukar bayanan matasan ne tukum kafin su san abin da za su yi da su.