Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta kira taron tsaro na gaggawa kan yawaitar hare-haren da ake kai wa ofisoshinta a jihohi daban-daban.
INEC ta kira taron ne bayan harin da aka kai ofisoshinta na jihohin Ogun da Osun a ranar Alhamis, wadanda su ne na 47 da aka kai wa mata daga 2019 zuwa yanzu.
Kwamishina Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a Kan Zabe an INEC, Festus Okoye, ya ce manya-manyan jami’an tsaro na hukumar ne za su halarci taron.
Ana sa ran Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro za halarci zaman da zai gudana a hedikwatar INEC da ke Abuja a ranar Juma’a.
Taron zai tattauna ne kan yadda za a dakile hare-haren, la’akar da kusatowar babban zaben shekarar 2023.
Wata majiya a hukumar ta fada wa wakilinmu cewa da gangan ake kai wa hukumar hare-haren domin a gurgunta ayyukanta.
Wata majiyar ta daban kuma ta danganta hare-haren da masu fafutukar kafa kasar Yaarbawa ta Oduduwa.
“Sun kai hari kan wani wuri mallakin sojin Najeriya a Jihar Ogun kwanan nan, inda suka kwashi makamai” in ji majiyar.