’Yan jarida a jihar Kano sun kirkiro wata kungiya da za ta daidaita al’amuran kafafen yada labarai na intanet.
An gudanar da zaben Shugabannin kungiyar ne a ranar Asabar, kuma shi ne karo na farko da aka samar da wata kungiya domin kula da kafafen watsa labarai na intanet a jihar.
- ’Yan aji dayan sakandare a Kano za su koma makaranta ran Litinin
- ‘Kwanan nan za a dawo da jigilar kasa da kasa a filayen jiragen Kano da Fatakwal’
Wadanda aka zaba a matsayin shugabannin kungiyar sun hada da, Hisham Habib daga News Tunnel, Shugaba; Nazifi Dawud daga DailyFocus, Mataimakin Shugaba; da Yakubu Salisu daga Metro Daily, Sakatare.
Sauran sun hada da Abbas Yusha’u na Nigerian Tracker, Mataimakin Sakatare; Mukhtar Yahaya Usman na Kano Focus, Sakataren Kudi; Zainab Mai Agogo daga White Blood Multimedia, Ma’aji; da Muhammad Buhari Abba daga Labarai24, Mai Binciken Kudi.
Zababbun shugabannin sabuwar kungiyar ana sa ran za a kaddamar da su a ranar Litinin, 16 ga Nuwamba.