✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kafa harsashin ginin kasuwar zamani a Patiskum

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya kafa ginin harsashen sabuwar kasuwar zamani a garin Potiskum.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya kafa ginin harsashen sabuwar kasuwar zamani a garin Potiskum na jihar.

Ana sa ran kammala ginin kasuwar wanda zai lashe kudaden da yawansu ya kai sama da Naira biliyan biyu da miliyan dari shida a cikin watanni 12 masu zuwa.

Gwamna Buni, yayin aza harsashin ginin kasuwar, ya ce makasudin gina kasuwar ta zamani shi ne bunkasa tattalin arzikin jihar Yobe da samar da guraben ayyukan yi ga al’ummar jihar.

Gwamnan ya ce akwai wasu kasuwannin makamantan wannan da yanzu haka ake ginawa a garin Damaturu da Gashua da Nguru dama wasu garuruwan, sai kuma aikin shimfida bututun samar da ruwan sha a wasu yankunan jihar.

Kazalika, gwamnan yace tuni gwamnatin jihar ta amince da ware sama da N195, 831,900 don biyan kudaden diyya a wuraren da aikin kasuwar ya shafa.

A nasa jawabin, shugaban Hadaddiyar Kungiyar ‘Yan kasuwar Potiskum, Nasiru Mato, ya mika godiyarsa ga gwamna Buni bisa kokarinsa na samar da kasuwar ta zamani.

Ya ce samar da kasuwar zai bunkasa harkokin kasuwanci a karamar hukumar ta Potiskum dama jihar baki daya.