✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kafa dokar hana Fulani shan barasa

Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin ya jagoranci wani taron hadin gwiwa tsakanin al’ummomin Fulani da Yarabawa na garin Igangan a Jihar Oyo da suka amince…

Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin ya jagoranci wani taron hadin gwiwa tsakanin al’ummomin Fulani da Yarabawa na garin Igangan a Jihar Oyo da suka amince da daukar matakin kafa dokar hana matasan Fulani shan barasa a dukkan gidaje da shagunan da ake sayar da giya a yankin.

daukar wannan mataki ya biyo bayan wani kazamin fada ne a tsakanin matasan Fulani da suka yi amfani da adduna da wukake da sanduna wajen sarar juna, inda suka jikkata junansu bayan sun yi tatil da barasa a garin na Igangan. Babu hasarar rayuka a wajen wannan fada amma da yawa daga cikinsu sun samu munanan raunuka da aka garzaya da su zuwa asibitocin gwamnati.

Sarkin na Sasa, wanda ya shugabanci zaman taron sasanci tsakanin bangarorin Fulanin da ke jayayya, yana tare ne da Sarkin Igangan, Asigangan, Oba Lasisi Adeoye da sauran shugabannin Fulanin yankin da suka tabbatar da cewa fadan ya samo asali ne daga gidan giya. Wannan ne ya sa a nan take aka amince da kafa wannan doka a wajen taron.

Da yake yi wa Aminiya bayanin sakamakon bayan taron, Sarkin Sasa ya ce: “Dattawan Fulanin Igangan ne suka nemi mu je mu sasanta al’amarin kafin ya kazanta. Na lura da irin matakan gwamnati a kan tsaron lafiyar jama’a, shi ne ya sa na hanzarta zuwa wannan gari, a inda muka zauna da Sarkin Ingangan da dattawan Fulani da shugabannin kungiyoyi da muka amince da kafa wannan doka ta hana matasan Fulani shiga gidajen giya a wannan yanki.

“Akwai ’yan sintiri da za su rika lekawa cikin gidajen sayar da barasa a wannan yanki domin tabbatar da aikin dokar. Kuma mun kafa kwamitin da zai tsara bayanan zaman namu domin mika sakamako da matsayinmu a kan wannan al’amari ga gwamnatin jihar.”

Ya kara da cewa, sun yi taron ne tare da wakilan rundunonin tsaro na soja da ’yan sanda da Sibil Difens. “Na umurci ’yan sanda su yi kyakkyawan bincike domin gano dukkan masu hannu wajen haddasa wannan fitina, a gurfanar da su gaban kotu domin hukunta su saboda ya zama darasi,” inji shi.  

Ya yi kira da a kafa irin wannan doka a ko’ina cikin kasa domin an gano cewa shaye-shayen giya da sauran abubuwan maye da matasan Fulani suke yi, shi ne yake ingiza su aikata miyagun abubuwa da ke tayar da hankalin jama’a.