Matasa a Jihar Neja sun kaddamar da zanga-zangar nuna adawa da matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya.
Matasan sun fara zanga-zangar ne a kan tituna, suna daga kwaleye masu dauke da rubutu a jikinsu da ke nuna bacin ransu kan halin tsadar rayuwa a kasar.
Rubutun jikin kwalayen sun hada da ‘tura ta kai bango’; ‘A soke tsare-tsere masu kuntata wa jama’a’; ‘Mu Ba Bayi Ba Ne A kasarmu’; ‘Ba Za Mu Jere Wannan Wahalhalun Ba’, ‘Dole A Dawo da tallafin man fetur’, da sauransu.
Masu zanga-zangar sun rika rera wakokin nuna adawa da gwamnati a yayin da suke tattaki a kan tituna.
- NAJERIYA A YAU: Shin Zanga-Zanga Na Tasiri A Najeriya?
- Zanga-Zanga: Kungiyar Furofesoshi Kiristoci a Arewa ta yi Allah wadai
Wakilinmu ya ga wasu daga cikin masu zanga-zangar a hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka yi yunkurin yin magana da su amma suka ki.
Gwamnonin tarayya da na jihohi suna yi yunkuri da dama na don dakatar da zanga-zangar, suna masu cewa zauna-gari-banza da makiya dimokuradiyya za su iya kwace ta.
A makon da ya gabata ne Gwamna Mohammed Bago na Jihar Neja ya ba wa al’ummar jihar da kayayyakin jin kai don hana zanga-zangar.
Ya sanar da biyan alawus din N20,000 ga ma’aikatan gwamnatin jihar da na kananan hukumomi.
Hakazalika ya ba da umarnin a gaggauta fito da ton 50,000 na hatsi iri-iri da za a sayar da su a rabin farashinsu don rage wahalhalun da tattalin arzikin kasar ke ciki.
A cewarsa, “Muna da sama da tan 100,000 na abinci a rumbun ajiyarmu, wanda daga ciki za mu fitar da metrik ton 50,000 a sayar a kan rabin farashin da yake yanzu.
“Kafin karshen shekara, za mu rage farashin kayan abinci da kashi 90 cikin 100, ”in ji shi a wani taro ganawa da al’umma.
Domin nuna jin dadinsu kan kokarin da suke yi na yaki da ’yan fashin daji da sauran miyagun ayyuka, gwamnan ya sanar da bai wa kowane shugaban hukumar tsaro a jihar kyautar Prado Jeep guda daya.