✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kaddamar da Gidauniyar Zakka da Wakafi a Gombe

An kaddamar da Gidauniyar Zakka da Wakafi a Jihar Gombe don wayar da kan mutane kan yadda ya kamata a tara kuma a raba zakka…

An kaddamar da Gidauniyar Zakka da Wakafi a Jihar Gombe don wayar da kan mutane kan yadda ya kamata a tara kuma a raba zakka yadda addinin Musulunci ya tanada.

A jawabin Shugaban Gudanarwar Gidauniyar Alhaji Abdullahi Abubakar Lamido, ya ce maaasudin kafa gidauniyar shi ne saboda sun lura wadansu Musulmi suna fitar da Zakka ba yadda Allah Ya shar’anta ba.

Alhaji Abdullahi Abubakar Lamido, ya ce jihohin Kano da Katsina da Jigawa da Sakkwato da Zamfara suna aiwatar da Zakkar ne da hadin kan masarautunsu amma a Jihar Gombe babu tsari tabbatacce wajen gudanar da Zakka shi ne suke son cike wannan gurbi.

Ya ce za su karbi zakka su raba ta ga wadanda suka dace da kuma fatar wanda aka bai wa shi ma zuwa wasu shekaru ya fitar ba wai a bai wa mutum wata shekara a ga yana da buakata ba.

“Wakafi kuma sadakatul jariya ce kowa zai iya yi amma Zakka ba kowa yake fitar da ita ba sai wanda dukiyarsa ta isa nisabi,” inji shi.

Malamin da ya gabatar da mukala kan yaki da fatara a wurin, Sheikh Dokta Bashir Aliyu Umar, ya ce fitar da zakka a bai wa wanda yake da buaata ma yaki ne da fatara.

Dokta Bashir Aliyu, ya ce talaka fakiri shi ne wanda yake da abin da zai ci amma bai ishe shi ba shi kuma miskini shi ne wanda bai da cin yau balle na gobe.Ya ce Annabi Muhammad (SAW) ya ce a nemi tsari da talauci, kuma ya jawo daga Alkur’ani Mai girma da take nuna cewa a nemi tsari da talauci.

Dokta Nura Abdullahi daga Jami’ar Bayero ta Kano, ya bukaci a hada kai da makarantun Islamiyya da na boko da kungiyoyi na iyayen yara da Kwamishinan Ilimi domin karfafa muhimmancin Wakafi.

Dokta Nura, ya ce idan yara suna zuwa makaranta a bullo da wani tsari na kati da za a rika saya don wakafi da za su iya saye daga kudin tara don su girma da abin a zuciyarsu.

A lokacin taron an an yi gwaji a karon farko na bai wa mata 30 tallafin Naira dubu goma-goma don yin sana’a.

Wadansu daga cikin zawarawan da suka amfana da tallafin sun yi yaba wa gidauniyar inda suka yi kira ga masu kudi da su hada kai da gidauniyar don fitar da zakka yadda ya dace.