✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbi soja yayin rikicin kabilanci a Gombe

Matasan sun ci karfin dakarun sojin ne lokacin da suke kokarin dakile harin.

Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Gombe sun ce an harbi wani soja tare da kone gidaje da dama, yayin da wasu kuma suka ji rauni a wani sabon rikicin kabilanci da ya barke a kauyen Nyuwar.

Garin dai na kan iyakar Jihar da takwararta ta Adamawa.

Wata majiya ta ce an harbi sojan ne yayin da yake kokarin dakile farmaki da matasan kabilar Waja suka kai wa mazauna yankin Nyuwar.

Amma an garzaya da shi wani asibitin da ba a bayyana sunansa ba, don ba shi agajin gaggawa.

A watan Afrilun bara, an zargi matasan kabilar ta Waja da kai wa ’yan kabilun Nyuwar da Jessu hari.

Rahotanni sun ce duk da kokarin dakile harin da jami’an tsaro suka yi, sai da matasan suka ci karfinsu.

Harin ya yi sanadin konewar gidaje da dama, yayin da mata da kananan yara suka tsere zuwa wasu garuruwa don neman dauki.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Gombe, ba ta magantu ba a kan harin.