✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An harbe sojoji biyu a Ebonyi

Wasu ’yan bindiga sun kashe sojoji biyu a wani shingen binciken ababen hawa da dakarun tsaro suka kafa a Karamar Hukumar Afikpo ta Arewa da…

Wasu ’yan bindiga sun kashe sojoji biyu a wani shingen binciken ababen hawa da dakarun tsaro suka kafa a Karamar Hukumar Afikpo ta Arewa da ke jihar Ebonyi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa wannan lamari ya faru ne da misalin karfe 9.00 na daren ranar Litinin da ta gabata.

“’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da bindigogin sojoji biyun da suka kashe,” a cewar majiyar rahoton.

Wata majiyar ta kuma bayyana cewa, bayan isowar ’yan bindigar shingen binciken ne sai sojoji suka tsayar da su domin bincikarsu amma suka bude musu wuta nan take.

“Mun shiga cikin wani yanayi mai cike da bakin ciki gami da damuwa bayan ’yan bindigar sun isa shingen binciken ababen hawa na Timber Shade da ke iyakar Ehugbo da Amasiri a cikin wata farar bas.

“Kamar yadda aka saba, sojojin sun tsayar da motar ne domin bincike sai kwatsam aka bude musu wuta, inda biyu daga cikin sojojin suka mutu nan take, ragowar kuma suka arce.

“Nan da nan yankin ya zama kufai yayin da sawun mutane ya dauke sabanin yadda ake kai-komo da hada-hadar mutane musamman ’yan kasuwa da manoma,” a cewar majiyar.

Sai dai har yanzu rundunar sojin bata bayar da wata sanarwa ba game da aukuwar harin, kuma babu wata kungiya da ta dauki alhaki a kansa.

Aminiya ta ruwaito cewa, wasu bata-gari sun banka wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi wuta a ranar Litinin da dare.

Akalla jami’an tsaron da ke gadin kotun biyu ne suka jikkata a yayin harin da aka kai da misalin karfe daya na daren ranar wanda aka kona wani sashe na ginin kotun.

Rahotanni sun ce bata-garin sun yi amfani da fetur ne wurin tayar da wutar wacce ta yi sanadiyyar konewar sassa da dama na kotun, ciki har da dakin adana bayanai da kuma ofishin jami’an tsaro.

Lokacin da wakilinmu ya ziyarci kotun da safiyar Talata, ya iske an girke motocin jami’an ’yan sanda guda uku a muhimman wurare na kotun.