✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbe dan jarida a Ibadan

An kashe dan jaridar ne a wani gidan rawa da ke Ibadan.

Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Oyo a ranar Lahadi ta tabbatar da kisan wani dan jarida, Titus Badejo, da aka fi sani da Ejanla, wanda aka harbe shi ranar Asabar da maraice.

Aminiya ta ruwaito cewa an kashe dan jaridar ne a wani gidan rawa da ke unguwar Oluyole cikin birnin Ibadan babban birnin Jihar Oyo da misalin karfe tara na dare.

Wakilinmu ya ce mutum hudu ne suka harbe dan jaridar kuma sun isa wajen a kan babura inda suka bude masa wuta.

Kisan dan jaridar na zuwa ne mako daya cif bayan ya yi bikin zagayowar ranar  haihuwarsa a dai wannan otel din da aka kashe shi.

Da yake tsokaci kan lamarin, kakakin ’yan sandan Jihar, Adewale Osifeso, ya fada wa ’yan jarida cewa an harbe mutumin ne a gaban wani gidan rawa da ke yankin Oluyole a birnin na Ibadan.

Ya ce tuni rundunar ta dukufa ka’in da na’in a wajen ganin ta gano musabbabin kisan gillar tare da bankado makasan.

%d bloggers like this: