✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta zanga-zanga ba tare da izini ba a Sudan

Shugaban Sudan Umar Al-Bashir ya sanar da haramta zanga-zanga da tafiya yajin aiki a kasar ba tare da samun izini yin haka ba. Rubutacciyar sanarwar…

Shugaban Sudan Umar Al-Bashir ya sanar da haramta zanga-zanga da tafiya yajin aiki a kasar ba tare da samun izini yin haka ba.

Rubutacciyar sanarwar da aka fitar daga Fadar Shugaban Kasar ta ce, bayan dokar ta-baci da Shugaba Al-Bashir ya yi a baya, ya sake fitar da wasu sababbin dokoki. Sababbin dokokin da aka fitar sun hada da na haramta wa ’yan kasar Sudan yin zanga-zanga ko yin yajin aiki ba tare da samun izini daga hukuma ba. Kuma jami’an tsaro za su iya neman kowane mutum a kowane waje. Sannan duk wasu kaya na haram da aka kama za a iya kwace su tare da gurfanar da mutane a gaban kotu.

A karkashin dokar ta-bacin da aka saka, an bai wa jami’an tsaro damar gurfanar da duk wadanda suka kama da aikata laifi a gaban kotu. Sannan bijire wa umarnin hukumomi da kuma lalata kayan gwamnati ko cin zarafin alamun kasa da rashin girmama kasa duk manyan laifuffuka ne.

Sannan za a hana buga duk wani labari da zai ci karo da kundin tsarin mulki ko ya saba wa bukatun kasa da na al’umma kamar yadda kafar labarai ta TRT ta ruwaito.

Haka saya ko sayar da kudaden waje a wuraren da gwamnati ba ta amince ba ya zama babban laifi kuma matafiya ba za su dauki sama da Dala dubu 3 a hannunsu ba yayin fita kasar waje.