Hukumomi a Mauritania sun haramta wa tsohon Shugaban Kasar Mohamed Ould Abdel Aziz, wanda ke fuskantar shari’a kan zargin cin hanci da rashawa, fita kasashen waje.
Rahotanni daga kasar na cewa a ranar Laraba jami’an tsaro suka hana tsohon shugaban yin balaguro, bayan ya isa filin tashi da saukar jiragen sama.
- Za a iya samun bullar Covid-19 fiye da yadda aka fuskanta a baya —NCDC
- Ba mu kai karar Shugaban INEC kotu ba —DSS
Ould Abdel Aziz ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ‘yan sandan siyasa ne suka hana shi fita daga kasar, duk da cewa babu wani takunkumi na shari’a da yake kansa.
Tsohon shugaban na Mauritania wanda ya karbe ikon kasar a juyin mulkin da aka yi a shekarar 2008, ya sauka a shekarar 2019 bayan yin wa’adi biyu akan kujera.
Mohamed Ould Ghazouani, wanda ya kasance tsohon Janar a rundunar sojin kasar, shine ya gaje shi
Mohamed Ould Abdel Aziz na fuskantar shari’a tare da wasu mutum 11 bisa zargin cin hanci da rashawa, azurta kansa da dukiyar kasar, tun daga lokacin da ya karbi mulki har zuwa lokacin da ya sauka.
Wadanda ake tuhuma tare da tsohon shugaban, za su gurfana a gaban kotu ranar 25 ga watan Janairu, a cewar Ma’aikatar Shari’a.