✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hana wata auren makadin garaya a Saudiyya

Wata kotu a Saudiyya ta yanke hukuncin hana wata mata auren masoyinta bayan da ’yan uwanta suka soki auren domin mutumin makadi ne. ’Yan uwan…

Wata kotu a Saudiyya ta yanke hukuncin hana wata mata auren masoyinta bayan da ’yan uwanta suka soki auren domin mutumin makadi ne.

’Yan uwan matar, wadda manajar banki ce, sun ki amince mata ta auri mutumin, wanda shi kuma malamin makaranta ne domin sun ce yana kada garayar ‘Oud’, lamarin da suka ce zai lalata mata tarbiyyarta ta addini.

Wata karamar kotu ce ta fara yanke hukunci, inda ta goyi bayansu, kuma wata babbar kotun kasar ta tabbatar da hukuncin bayan da matar ta daukaka kara.

Wadansu mutanen kasar mai bin addini sau-da-kafa na kallon kida da waka a matsayin haramtaccen abu.

Amma duk da haka, Saudiyya na da tarihi mai karfi a bangaren kade-kade da wake-wake, har ma da masu amfani da garayar ta oud.

Akan kuma kyale mawaka daga kasashen Turai su yi wasanni a kasar kamar yadda BBC ya ruwaito.

Batun ya ja hankalin mutane a shafukan sada zumunta, bayan da wani lauyan Saudiyya mai suna Abdul Rahman al-Lahim ya tattauna a kan batun a wani bidiyo da ya saka a shafinsa na Snapchat

Ya ce matar, wadda ’yar asalin Unaiza ce da ke yankin Kassim ta nemi ya shigar da kara shekara biyu da suka gabata, inda take karar ’yan uwanta maza saboda sun ki amincewa ta auri wani mutumin da “ya taba kada garayar oud, wanda a ganinsu ya aikata zunubi ne.”

Lauya Lahim ya ce ba a bai wa mutumin damar ya kare kansa a gaban kotun ba.

Matar ta sanar da jaridar Okaza cewa har yanzu tana son auren mutumin, wanda ta bayyana shi a matsayin “mai bin addini sau-da-kafa, kuma mai kyan hali.”

Ta ce za ta nemi Kotun Kolin Kasar – wato Masarautan Kasar ke nan – su sake duba batun.

A karkashin dokokin Saudiyya, wajibi ne mata kanana da manyansu su nemi izinin wani dan uwansu namiji – kamar miji ko mahaifi ko da kafin ta iya karbar fasfo, ko yin tafiya zuwa kasar waje, ko yin karatu a kasar waje ko yin aure ko ma komawa gida daga kurkuku bayan ta kammala zaman gidan kaso.