Wasu ’yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Muhammad Bunu, inda suka kashe mutane uku suka yi awon gaba da wasu.
Wakilinmu ya tabbatar mana da cewa an sace mutane ukun da aka sace sun hada da Sarkin Gidan Masarautar Zurmi, Alhaji Yusuf Buhari da wani mai shayi da ke kusa da fada, da wani mutum guda.
Mazauna yankin sun ce bayan fadar sarkin, maharan na daren Laraba, sun kai hari gidan tsohon shugaban mulkin soja na Jihar Nasarawa, kuma tsohon ministan muhalli a gwamnatin Olusegun Obasanjo, Kanar Bala Muhammad Mande mai ritaya.
Shaidu sun ce a lokacin da aka kai harin Kanar Mande mai ritaya ba ya gida, amma Sarkin Zurmi na cikin fadarsa lokacin da ’yan bindigar suka kaddamar da harin.
- Kwastam ta mika wa DSS nakiyoyi 6,240 da aka kama a Kebbi
- Ainihin Dalilin Wahalar Man Fetur A Najeriya
A yayin harin, ’yan bindigar sun lalata turken sadarwa, sannan suka kone wasu injina guda biyu da ke kusa da fadar sarkin.
Wani mazaunin garin da ya nemi a boya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa, daga shigowar maharan garin suka nufi gidan sarkin suka buɗe wuta a babbar kofar gidan a kokarinsu na samun shiga fadar domin sace sarkin.
Ya ce: “Inda Allah Ya kiyaye shi ne, an kulle kofar, amma ba don haka ba, da sun samu shiga cikin fadar, domin shi suka zo nema”.
Ya ce a kwanakin baya ma ’yan bindigar sun kai wa sarkin farmaki, amma sai Allah Ya kiyaye shi.
“A zahirin gaskiya ma, sarki ya dawo gari ne a ranar Litinin bayan yunkurin sace shi na farko bai yi nasara ba.
“A sirrance aka sa sarkin ya koma Gusau, inda ya shafe mako guda a can,” in ji shi.
Wani mazaunin garin kuma ya ce da maharan suka kasa samun shiga fadar, sai suka koma gidan tsohon sojan, suka yi ta harbe-harbe a kofar gidan, suka lalata abubbuwa da yawa.
Muhammad Inuwa, wani ɗan Zurmi ya ce yana shirin mayar da iyalansa Gusau saboda ba zai iya jure halin baƙin ciki da tashin hankalin da mazauna yankin ke ciki sakamakon hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa ba.
Ya ce: “Na gaji…Muna cikin bala’i da tawayar tattalin arziki ga kuma tashin hankalin ’yan fashi. Nauyin ya yi min yawa. Ba zan iya jurewa ba.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalijan, ya tabbatar da faruwar harin amma amma ya ce ba shi da masaniyar cewa an kashe wasu mutane.
Sai dai ya tabbatar da cewa ’yan bindigar sun sace daya daga cikin dogaron Sarkin Zurmi.
“Ba a fadar sarki a ka sace shi ba, a cikin gari ne aka ɗauke shi,” in ji kwamshinan ’yan sandan.