✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gutsure kan wani dan lwallo a Brazil

Rahotanni da ke fitowa daga Brazil sun nuna wadansu bata-gari da ba a san ko su wane ne ba sun kashe dan lwallon kulob din…

Rahotanni da ke fitowa daga Brazil sun nuna wadansu bata-gari da ba a san ko su wane ne ba sun kashe dan lwallon kulob din Sao Paolo Daniel Correa Freitas ta hanyar daddatsa shi sannan suka yanke kan kafin su jefar da gawarsa a gefen titi sannna suka arce ba tare da an kama su ba.

Al’amarin ya faru ne a ranar Asabar da ta wuce da dare kamar yadda rahoton da kafar watsa labarai ta Naij.com ta kalato.   Ta ce kawo yanzu ba a san dalilin da ya sa mutanen suka kashe dan lwallon ba.

Matashi Daniel Freitas dan shekara 24 ya buga wa kulob da dama lwallo a Brazil da suka hada da Cruzeiro da Botofogo a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015 kafin ya canza shela zuwa kulob din Sao Paolo a bana (2018).

Daga nan ne kulob din ya aika shi zuwa Sao Bento a matsayin aro kuma wasa biyu kacal marigayin ya yi kafin ya gamu da ajalinsa.

Tuni mahukunta kulob din Sao Poalo suka aika da salon ta’aziyya ga iyalan mamacin a bisa wannan abin tashin hankali da ya samu dan lwallonsu.

Jami’an tsaro da ke yankin Parana da al’amarin ya faru tuni shiga shiga bincike don zalulo wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Al’amarin kashe mutane a Brazil ba sabon al’amari ba ne, don an sha samun rahotannin kashe bayin Allah a sassa daban-daban na lasar