✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da matar da ta raba fetur a wajen biki a gaban kotu

Kotun dai ta bayar da belinta kan kudi miliyan biyu

Matar nan da ta raba man fetur a wajen biki a Jihar Legas, Misis Ogbulu Chindinma Pear, ta gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Oshodi a Jihar.

Ana dai zargin matar da yunkurin jefa rayuwar mutane cikin hatsari ta hanyar raba jarkokin man fetur a wurin wani taron bikin nadin sarauta da aka mata sati biyu da suka shude.

Alkalin kotun majistaren, Kehinde Ogundare, ya ce laifin ya saba da sashe na 251(1), 168 (1), 244 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Legas.

Amma alkalin ya ba da belinta kan kudi Naira miliyan biyu da kuma gabatar da mutum biyu da za su tsaya mata a kotun.

Alkalin kotun ya kuma ba da umarnin tabbatar da adireshin wadanda suka tsaya mata tare da tabbatar da cewa sun nuna takardun hujjar biyan gwamnatin Legas haraji na tsawon shekara uku da ta gabata.

Daga bisani dai an dage zaman shari’ar zuwa ranar 24 ga Maris, 2022.

Idan za a iya tunawa wani bidiyo ya bulla a shafin Twitter, inda ya nuna yadda ake rabon man fetur a matsayin kayan kyauta, lamarin da ya harzuka mutane da dama a daidai lokacin da ake fama da karancinsa a fadin Najeriya.

Tun bayan bullar bidiyon gwamnatin Jihar Legas ta kuduri aniyar gudanar da kwarya-kwaryar bincike kan lamarin.